Sama da fararen hula 30, da suka hada da yara kanana 10, aka hallaka a ranakun 29 da kuma 30 ga watan Oktoba, a sakamkon hare-haren da aka kaddamar a yammacin birnin Aleppo dake karkashin ikon gwamnatin kasar Syria.
Ofishin babban kwamishinan hukumar kare hakkin bil adama ta MDD wato OHCHR, ya yi gargadin cewa, rashin mutunta dokokin kare hakkin dan Adam na kasa da kasa da mayakan 'yan tawayen ke yi, inda suke hallaka fararen hula masu yawan gaske tamkar aikata laifukan yaki ne.
A wata sanarwar da mai magana da ofishin na OHCHR Ravina Shamdasani ta fitar, ta ce rahotannin da aka samu game da yin amfani da makamai masu linzami da kuma tankokin yaki makare da ababan fashewa da aka yi amfani da su a yankunan wanda ya haddasa raba mutane sama da miliyan 1 da muhallansu ba batu ne da za'a lamunta ba, kuma tamkar aikata laifukan yaki ne.
A cewar rahoton, mayakan 'yan tawaye dake rike da ikon gabashin lardin, sun kwace ikon yankunan dake makwabtaka da Salah al-Din, al-Shahbaa, al-Zahraa da al-Hamadaniya inda suke kaddamar da hare-hare ta hanyar amfani da rokoki da sauran abubuwan fashewa.(Ahmad)