A yayin shawarwarin, Sergei Lavrov ya ce, kasashen uku a shirye suke su yi iyakar kokarinsu don yaki da kungiyoyin ta'addanci dake Syria, kana sun tsara wani shiri game da irin matakan da suka wajaba a dauka cikin kwanaki masu zuwa, domin murkushe kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi na IS, da Jabhat Fateh al-Sham, kuma a cewarsu wannan wani muhimmin aiki ne dake gabansu.
Baya ga haka, Sergei Lavrov, ya nuna cewa, kwanan baya sojojin gwamnatin Iraki sun kaddamar da hare hare a birnin Mosul, hakan ya sa mai yiwuwa ne 'yan ta'addan dake wurin za su canja wurin yaki zuwa Syria. (Bilkisu)