in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana ci gaba da rikice-rikice a birnin Aleppo na Syria
2016-10-30 13:19:56 cri

Sojojin gwamnatin kasar Syria sun kwato wasu wuraren dake arewancin birnin Aleppo bayan wani babban gumurzu da suka yi da dakaru masu adawa da gwamnati, amma duk da haka ana ci gaba da samun rikice-rikice a birnin na Aleppo.

Bisa labarin da aka samu daga kungiyar sa ido kan yanayin hakkin dan Adam na kasar Syria dake da hedkwata a birnin London na kasar Birtaniya, an ce, an yi masuyar wuta mafi tsanani a garin Assad dake yammacin birnin Aleppo a wannan rana, inda dakarun dake adawa da gwamnati suka sami nasarar yaki, tare kuma da yiwa wani sansanin sojojin gwamnati kawanya a wani wuri.

Bugu da kari, an ce, cikin kwanaki biyu da suka gabata, dakaru sun yi ta kai hare-hare a wasu matsugunan jama'a dake birnin Aleppo, lamarin da ya haddasa rasuwar mutane a kalla guda 13, yayin da 106 suka jikkata.

A watan Satumba na bana, sojojin gwamnatin kasar Syria sun sami ci gaba kan matakan soja da suka dauka a birnin Aleppo, inda suka cimma nasarar yin kawanya kan wuraren dake karkashin ikon dakaru masu adawa a gabashin birnin Aleppo. Sa'an nan, daga ranar 20 zuwa ranar 22 ga watan nan da muke ciki, sojojin gwamnatin kasar sun dakatar da bude wuta na kwanaki uku a birnin Aleppo, amma, an ci gaba da tashe hare-hare a tsakanin sojojin gwamnati da dakarun dake adawa bayan wadannan kwanaki uku. Kaza lika, a ranar 28 ga wata, wasu kungiyoyin adawa sun kai miyagun hare-hare a wuraren dake karkashin shugabancin gwamantin kasar dake gabashin birnin Aleppo domin murkushe kawanyar da sojojin gwamnatin suka yi musu a yankin. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China