Cikin sakonsa, mista Ban ya ce yana farin ciki ganin yadda aka zartas da kudurin ba tare da samun sabanin ra'ayi ba. A cewarsa, yadda aka zama tsintsiya madaurinki daya a wannan karo zai taka muhimmiyar rawa wajen daidaita al'amura a zirin Koriya, gami da sauran sassan duniya.
Ya fara daga watan Janairun bana, kasar Koriya ta Arewa ta yi gwajin makaman nukiliyarta har sau 2, gami da gwajin makamai masu linzami a kalla har sau 25. Irin yanayin da kasar take ciki ya sa kwamitin sulhu na MDD ya kira taron gaggawa karo na 9 cikin wannan shekara, don samar da dabarar da za a dauka ta yadda za a kau da matsalar nukiliya a zirin Koriya. (Bello Wang)