in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin kasar Sin ya jaddada ce dole ne a bi manufar daidaita batun Sham ta hanyar siyasa
2016-12-01 10:24:41 cri
A jiya Laraba, Mr. Wu Haitao, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD ya nuna cewa, idan ana son sassauta matsanancin halin da ake ciki a yankin Aleppo na kasar Sham, dole ne a bi manufar daidaita batun Sham ta hanyar siyasa a karkashin inuwar MDD bisa hakikanin halin da ake ciki a kasar.

A jiya ne kwamitin sulhu na MDD ya shirya wani taro kan batun Sham a fili, inda aka saurari rahotonnin da Mr. Staffan de Mistura, wakilin musamman na babban sakataren MDD kan batun Sham da sauran mutane da suka gabatar game da halin da ake ciki a yankin Aleppo.

A cikin jawabinsa, Mr. Wu Haitao ya ce, a 'yan watannin nan, halin da ake ciki a wasu yankuna, ciki har da yankin Aleppo na kasar Sham ya kara tsananta, halin jin kai ma yana ta lalacewa. Gamayyar kasa da kasa tana mai da hankali sosai, kuma bangaren Sin na nuna tausayinsa ga al'ummomin Sham wadanda suke shan wahalhalu, kuma ya zargi dukkan hare-haren da ake kai wa farar hula da ayyukan yau da kullum nasu.

Wu Haitao ya kara da cewa, ya kamata gamayyar kasa da kasa ta yi kokarin daidaita ayyukan tsagaita bude wuta, yin shawarwarin siyasa, samar da taimakon jin kai da dakile ta'addanci, da kuma ta bukaci bangarori daban daban na Sham da su hanzarta dakatar da matakan yaki da juna domin sassauta matsanancin halin da ake ciki a yankunan kasar, ciki har da yankin Aleppo. Bugu da kari, dole ne a tsaya kan matsayin neman matsaya daya kan dukkan batutuwan da abin ya shafa ta hanyar yin shawarwarin siyasa. A waje daya kuma, dole ne a kara samar da taimakon jin kai a yankin Aleppo. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China