Babban sakataren Majalisar Ban Ki-moon ya yi jawabi wajen bikin cewa, rikici tsakanin Isra'ila da Falasdinu tamkar wani gyambo ne wanda ya dade ya ki warkewa, tare da sanadiyyar dauki-ba-dadi a daukacin zirin gabas ta tsakiya. A shekarun baya, shawarwari karo 2 da Isra'ila da Falasdinu suka yi duk sun yi zub da ciki, har ma an samu abkuwar fadace-fadace yayin shawarwarin, lamarin da ya haddasa mutuwar mutane fiye da dubu 1, galibinsu fararen hula 'yan Falasdinu.
A cewar Ban Ki-moon, za a shiga shekara ta 50 ne bayan da bangaren Isra'ila ya mamaye harabar Falasdinu, amma har zuwa yanzu an kasa ganin alamar cimma daidaito tsakanin bangarorin 2. A yanzu haka, kamata ya yi, gamayyar kasa da kasa su bayyana niyyarsu ta taimakawa bangarorin Isra'ila da Falasdinu don su sake shimfida imani tsakaninsu, da samar da damar gudanar da shawarwari.(Bello Wang)