in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin Sin ya bukaci hadin gwiwa tsakanin kungiyoyin don tunkarar mayan kalubaloli
2016-11-19 11:57:51 cri
Wakilin kasar Sin a MDD ya bukaci a samar da kyakkyawan hadin kai tsakanin MDD da kungiyar tarayyar Afrika AU, domin tunkarar manyan kalubaloli dake addabar sassan duniya.

Liu Jieyi, wakilin Sin na dindindin a MDD, ya yi wannan kira ne a lokacin taron kwamatin sulhun MDD game da batun hadin kai tsakanin MDD da AU.

Liu, ya ce, AU tana da muhimmiyar rawa da zata taka wajen warware manyan kalubalolin dake addabar nahiyar Afrika, kasancewar tana da kyakkyawar kwarewa da kuma dabarun warware matsaloli ta hanyar tattaunawa, kuma ita ce hukumar dake da dangantaka ta kut da kut da al'ummomin nahiyar Afrika, da kuma masaniya game da tarihi da al'adun mazauna nahiyar.

Ya kara da cewa, kasar Sin tana goyon bayan MDD wajen sauraron muhimman batutuwa da suka shafi Afrika, tare da taka rawar a zo a gani wajen warware duk wata takaddama da ta taso a nahiyar ta hanyar tattaunawar siyasa.

Liu, ya ce kasar Sin tana daukar dangantakar dake tsakaninta da AU da muhimmanci, kuma za ta cigaba da shiga a dama da ita cikin shirin wanzar da zaman lafiya na MDD a Afrika, kana za ta taimakawa kasashen nahiyar Afrikan wajen samar da tsaron kasa, da yaki da ta'addanci, da harkokin shigi da fici da na hukumar kwastam.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China