Karewa da bunkasa 'yancin mata sun kasance nauyin da ya rataya ga kowa a Afrika, in ji Aisha L. Abdullahi, shugabar reshen harkokin siyasa na kwamitin kungiyar tarayyar Afrika (AU), a ranar Alhamis a yayin wani taron manema labarai a Kigali a dabra da babban taron AU karo na 27.
Wannan damuwa ta tarayyar Afrika na bayyana zabin taken wannan dandali, wato "Shekarar 2016: Shekarar kare 'yancin dan adam, tare da mai da hankali musammun ma kan 'yancin mata".
A ganin madam Aisha L. Abdullahi, kungiyar AU tana bukatar fadakar da tunanin mutane da kuma tunatar da masu fadi a ji na Afrika kan nauyin da ya rataya kansu game da mata, musammun ma kare su daga duk wasu nau'o'in cin zarafi da nuna bambanci. A cewar shugaban reshen harkokin siyasa na kwamitin AU, wannan ya zama abu mai muhimmanci, duk da cewar akwai dokoki da dama da aka tanada kan wannan batu kamar yarjejeniyoyi da kudurori, ana cin karo da karuwar tashe tashen hankali da keta hakkin mata a nahiyar. Wannan matsala na ci gaba tsananta tare da karuwar guguwar kaifin kishin addinai.
Lamarin ya nuna babban gibi a cikin cin moriya baki daya na wadannan 'yanci na mata, ana fama da kalubalolin daidaici tsakaninsu da maza. (Maman Ada)