in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Muhimman labarai daga wasu jaridun Najeriya(20161125)
2016-11-25 19:20:32 cri

Shugaban majalisar dattawan Najeriya Bukoka Saraki ya bayyana a jiya Alhamis ce, majalisar tana fatan kammala gyaran kudin tsarin mulkin kasar zuwa watan Janairun shekara mai zuwa.(Daliy Trust)

A wani labarin kuma majalisar dattawan Najeriyar ta ce, ta gaji yadda ake kirkiro dokoki ba tare da ganin ana aiwartar da su yadda ya kamata ba. A saboda haka shugaban majalisar dattawan ya jaddada bukatar hada kirfi da karfe wajen ganin an kawo karshen wannan lamari.(Vanguard)

Asusun kudaden ajiyar ketare na Najeriya ya karu da dala miliyan 589 a 'yan makonnin da suka gabata, duk da bukatar da ake da ita.

Yanzu haka akwai kudade da yawansu ya kai dala biliyan 24.49, sabanin dala biliyan 23.91 da ke cikin asusun a makonnin hudun da suka gaba, adadin dake wakiltar karuwar kashi 2.5 cikin 100.(The Guardian)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China