in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya: An cafke tsoffin 'yan sanda 9 da ake zargi da sace mutane da sace-sace
2016-11-23 11:11:25 cri

Gwamnatin Najeriya ta cafke wasu tsoffin 'yan sanda 9 da ake zargi da taimakawa da goyon bayan satar dabbobi, yin fashi da kuma sace mutane a arewa maso gabashin Najeriya.

An yanke wa wadanda ake zargin hukuncin ladabtarwar na cikin gida bisa ga munin laifukkansu, in ji Don Awunah, kakakin 'yan sandan Najeriya, a yayin wani taron manema labarai a ranar Talata a Abuja, babban birnin Najeriya.

Haka kuma, ya bayyana cewa kame-kame, da amsa tambayoyi da ma amincewar laifin wadannan tsoffin 'yan sanda sun taimaka wajen cafke wasu mutane goma sha tara da ake zargi da sanya hannu kan bindigogi da albarusai da dama.

Mista Awunah ya bayyana cewa, an gano bindigogi kirar AK47 guda 14, da doguwar bindiga guda, da bindiga kirar gargajiya guda, da kwalayen albarusai 363 na bindigar AK47, da albarusai na bindigar K2 guda 71 da kwalayen harsashi 25.

Haka kuma, mista Awunah ya bayyana cewa, wani da ake zargi da fashi da makamai, Hod Adamu, ya shiga hannun 'yan sanda a cikin watan Oktoba a cikin jihar Adamawa. Inda ya kara da cewa, jami'an 'yan sandan da ake zargi za a gabatar da su gaban kotu nan gaba. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China