in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Muhimman labarai daga wasu jaridun Najeriya (20161124)
2016-11-24 20:21:10 cri
Gwamnatin tarayyar Najeriya tana shirin ragewa bangaren masana'antun samar da kayayyakin kasar harajin da yake biya, a wani mataki na saukaka wa musu masana'antu matsin tattalin arzikin da ake fuskanta a kasar.

Ministar kudin kasar Kemi Adeosun wadda ta bayyana hakan a jiya Laraba, ta ce, ragin biyan harajin wani bangare ne na matakan da gwamnati ta bullo da su da nufin ragewa bangaren masana'antun tasirin rashin kudaden musaya.(The Punch)

A jiya Laraba ne tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya yi kira ga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da ya magance kalubalen da kasar take fuskanta sakamakon matsalar tattalin arzikin da kasar ta tsinci kanta a ciki. Yana mai cewa, zuba ido kadai, ko wasu suddabaru ba za su magance halin da kasar ke ciki ba.

Haka kuma Obasanjo ya tofa albarkacinsa game da wasu batutuwa da suka hada da cin hanci da shirin gwamnati na karbo rance daga ketare da matsin tattalin arzikin da kasar ta ke ciki da sauransu. Ya kuma yabawa matakan gwamnati na yaki da cin hanci, amma kuma ya ce, gwamnati ba ta tsara manufofin da suka dace game da magance halin da kasar ta ke ciki ba.(Vanguard)

Kungiyar kare hakkin bil-Adam ta Amnesty International ta zargi sojojin Najeriya da halaka masu zanza-zangar lumana a kalla 150 a yankin Biafra da ke kudu maso gabashin kasar.

Kungiyar ta fitar da hotunan bidiyo 87 da wasu hotuna 122 da shaidun gani da ido 146 wadanda ke tabbatar da yadda sojojin Najeriya suka yi amfani da harsasai na zahiri kan taron jama'a tsakanin watan Agustan shekarar 2015 da watan Agustan shekarar 2016 ba tare da yi musu wani gargadi ba.(The Guardian) (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China