in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya za ta takaita kudin ruwa zuwa kashi 14 cikin 100 duk da matsin tattalin arziki da take ciki
2016-11-23 10:11:00 cri

Gwamnatin Najeriya ta yanke shawarar takaita adadin kudin ruwa a kasar zuwa kashi 14 cikin 100, duk da irin halin matsin tattalin arziki da kasar ke fama da shi.

Kwamitin tsara sha'anin kudin kasar ne ya amince da wannan mataki, bayan wata ganawar da ya gudanar ta tsawon kwanaki biyu a Abuja, babban birnin kasar, inda nan take kwamitin ya kada kuri'ar amincewa da kashi 22.5 bisa 100 da kuma kashi 30 bisa 100.

Gwamnan babban bankin kasar Godwin Emefiele, ya sheda wa 'yan jaridu cewa, masu tsara dabaru game da sha'anin kudaden kasar sun dauki wannan mataki ne bayan yin nazari kan irin hadarin da rage adadin kudin ruwan zai iya haifarwa ga tattalin arzikin kasar.

Sakamakon halin matsin tattalin arzikin da kasar ke fuskanta, ya sa masu tsara al'amuran kudin kasar suka yi watsi da irin shawarwarin da kwararru a harkokin kudi suka bayar na rage adadin kudin ruwan, domin baiwa gwamnatin kasar damar samun rance na cikin gida don habaka tattalin arikin kasar ba tare da kara adadin kudaden basuka na ayyukan ba da hidima ba.

Shugaban babban bankin ya ce, kiraye-kiraye game da rage adadin kudin ruwan da ake ta yi, kuskure ne, domin yin hakan zai iya haifar da rashin tabbas game da bunkasuwar al'amura a hukumomin gwamnati da masu zaman kansu a kasar. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China