Maikanti Baru, shi ne manajan daraktan kamfanin mai na kasar NNPC, ya tabbatar da hakan ga 'yan jaridu a Abuja, bayan kaddamar da tallar kwangilar aikin hako man kasar na shekarar 2016/2017.
Ya ce albarkatun man Najeriyar ba abin yarwa ba ne, kuma yana matukar jan hankullan 'yan kasuwar dake aikin tace danyen mai, saboda kyakkyawan yanayin da man yake da shi.
Baru, ya kara da cewa, akwai abubuwa masu daraja da ake fitarwa daga danyen man kasar, hakan ne ya sa yake da farin jini a kasuwannin duniya.
Najeriya tana hako gangar danyen mai dubu 600 ne a kullum tun bayan hare haren farfasa bututun man kasar lamarin da ke haifar da tafiyar hawainiya wajen hako danyen man kasar.(Ahmad Fagam)