in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kashe 'yan sanda 128 cikin watanni 3 a Najeriya
2016-11-24 09:34:53 cri

Babban sifeton 'yan sandan Najeriya Ibrahim Idris, ya ce kimanin 'yan sandan kasar 128 ne aka hallaka a lokacin da suke bakin aiki cikin watanni 3 da suka gabata.

Jami'in ya ce 'yan sandan sun gamu da ajalinsu ne a lokacin da suke kokarin dakile hare hare da kuma tabbatar da bin doka da oda a sassan kasar dabam dabam.

Cikin wata sanarwa da ta iske kamfanin dillanci labarai na Xinhua, sifeton 'yan sandan ya ce, wasu daga cikin jami'an nasu sun mutu ne a lokacin da wasu 'yan bindiga suka afkawa wasu yankunan jihar Zamfara a shiyyar arewa maso yammacin kasar, da jihar Anambara da ke kudu maso gabashin kasar, da kuma dakile barnar tsagerun Niger Delta a gabar teku na Okrika dake jihar Rivers mai arzikin mai.

Ya ce ana cigaba da daukar matakai domin kawo karshen hallaka jami'an 'yan sandan Najeriyar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China