in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Muhimman labarai daga wasu jaridun Najeriya
2016-11-23 19:24:12 cri
Kwamitin kula da manufofin kudi na babban bankin Najeriya ya ce, hanya daya tilo ta farfado da tattalin arzikin kasar, ita ce aiwatar da manufofin da aka tsara sau da kafa.

Wannan nema ya sa kwamitin ya yanke shawara tsayar da kashi 14 cikin 100 na kudin ruwa a matsayin daya daga matakan farfado da tattalin arzikin kasar da gwamnatin ta tsara. (The Guardian)

A jiya Talata ne kuma kwamitin kula da manufofin kudi na babban bankin kasar ya yi kira ga mahukuntan kasar, da su gaggauta kimanta yawan basussukanta na cikin gida kana su bullo da matakan biyan wadannan basussuka.

Kwamitin ya kuma gargadi gwamnatin cewa, tarin basussukan da ake bin sassan tattalin arzikin kasar, sun gurgunta harkokin kasuwanci. (The Punch)

Karamin ministan albarkatun man fetur na Najeriya Ibe Kachukwu ya bayyana cewa, yawan man da kasar take hakowa ya karu da kimanin ganga miliyan 1.9 a kowace rana. Sai dai kuma yadda tsagerun Niger Delta ke barnata bututan mai, ya sa yawan man da kasar take hakowa ya yi kasa zuwa ganga 900,000 daga ganga miliyan 2.2 da ta yi hasashen hakowa a kowace rana kamar yadda ta sanya a kasafin kudinta na shekarar 2016. (Vanguard)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China