in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Muhimman labarai daga wasu jaridun Najeriya(20161121)
2016-11-21 20:03:21 cri

Nan ba da dadewa ba shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya zai sake turawa majalisar dattawan kasar sunayen mutanen da ake son nadawa a matsayin jadaku, bayan da a makon da ya gabata majalisar ta yi watsi da sunayen mutane 46 wadanda ta ce, ba su da kwarewa a aikin jakadanci tun da farko shugaba Buhari ya mika mata don neman amincewarta.(The Punch)

Batutuwan da suka shafi matsalar musayar kudaden ketare, tsadar farashin kayayyakin masarufi da kudin ruwan da ake biya na kudaden rance da bankunan ke bayarwa, su ne abubuwa da masu tsara manufofin kudi za su mayar da hankali a yayin tattaunawarsu a yau.

Sai dai kuma babban bankin Najeriya ya ce, kudin ruwan da yake karba ba zai yi kasa da kashi 10 cikin 100 ba, kamar yadda ya tsara cikin watanni 12 da suka gabata wato kashi 12 cikin 100 a watan Maris na shekarar 2016 da kuma kashi 14 cikin 100 tun a watan Afrilun.(The Guardian)

Tawagar 'yan wasan kwallon kafan mata ta Najeriya a gasar cin kofin kwallon kafan mata na kasashen Afirka, ta fara gasar da kafar dama, inda ta doke kasar Mali da ci 6 da nema a wasan da suka buga jiya Lahadi a filin wasa na Stade Munipal de Lombe.(Vanguard)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China