in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Muhimman labarai daga wasu jaridun Najeriya(20161122)
2016-11-22 19:16:51 cri

A jiya ne hukumar kididdiga ta Najeriya ta fitar da wasu alkaluma da ke nuna cewa, daga watan Yuli zuwa Satumban wannan shekara, kayayyaki da sauran harkokin hidima da ake samarwa a cikin kasar sun yi kasa, sakamakon koma-bayan tattalin arzikin da kasar take fuskanta.

Bugu da kari, su ma kamfanoni da sauran sassan tattalin arzikin kasar, ba sa samar da adadin abubuwan da suka saba samarwa, saboda raguwar yawan man da kasar ta saba hakowa da kuma karancin kudaden musaya na ketare da kamfanonin ke fuskanta.(Vanguard)

A yau Talata ne gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa, yadda ake barnata na'urorin man fetur da iskar gas a yankin Niger Delta, suna daga cikin dalilan da suka haddasa koma-bayan tattalin arzikin kasar a rubu'i na uku na wannan shekara.

Tawagar kula da harkokin tattalin arzikin kasar karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasar Yemi Osinbajo ta gano cewa, yadda ragowar sassan tattalin arzikin kasar suke ci gaba da dogara kan bangaren mai da iskar gas, shi ma yana daga cikin dalilan da suka sanya tattalin arzikin kasar shiga halin da yake ciki a halin yanzu.(Daliy Trust)

A jiya Litinin ne a birnin Maiduguri, fadar mulkin jihar Borno, babban hafsan sojojin kasa na Najeriya, Laftana janar Tukur Buratai, ya gabatar da sunaye da hotunan mayakan Boko Haram 55 da ake nema ruwa a jallo, ciki har da jagoransu, Abubakar Shekau.(The Punch) (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China