Gwamnatin Najeriya ta ayyana shirinta na sauya fasalin sashen albarkatun man kasar, a wani mataki na inganta tattalin arzikin kasar.
Cikin wani rahoto da karamin ministan man kasar Ibe Kachikwu ya gabatar, ya ce gwamnatin na duba yiwuwar fadada hanyoyin raya tattalin arziki wanda bai shafi hada-hadar mai ba, a gabar da farashin man ke tangal tangal a kasuwannin duniya.
Mr. Kachikwu ya ce, gwamnatin na fatan karkata akalarta zuwa sashen albarkatun iskar gas, duba da tarin iskar gas din da Najeriyar take da shi.
Rahoton ya kuma bayyana aniyar gwamnatin na aiwatar da matakan da za su ba da damar inganta hada-hada a sashen na albarkatun mai yadda ya kamata, ciki had da batun samar da hanyoyin sarrafa sinadarai da ake samu daga gurbataccen mai.(Saminu)