in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar ma'aikatan man fetur a Najeriya sun yi watsi da batun sayar da matatun man kasar
2016-11-16 10:19:11 cri

Kungiyar ma'aikatan man fetur da iskar gas na Najeriya wato (NUPENG), ta ce ba za ta amince da yunkurin sayar da matatun man kasar ba tare da cikakkiyar tuntubar kungiyoyin 'yan kwadago a bangaren man fetur na kasar ba.

Tokunbo Korodo, shi ne shugaban kungiyar NUPENG na shiyyar kudu maso yammacin kasar, ya sheda wa 'yan jaridu a Legas cewa, ba za su zuba ido suna gani a sayar da matatun man kasar ba tare da cikakkiyar tuntubar kungiyar ba.

A ranar 13 ga wannan watan ne ma'aikatan kamfanin man Najeriyar suka bayyana cewa, ba za su amince da duk wani yunkurin gwamnatin kasar na sayar da wasu sassa na kamfanin man kasar wato NNPC ba.

Martanin dai ya zo ne bayan da gwamnatin kasar ta ambata cewa, za ta sayar da wasu daga cikin matatun man kasar da nufin bunkasa hanyoyin samun kudin shigar kasa.(Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China