Shugaban ya bayyana hakan ne a ranar Talata lokacin da ya ke jawabi a babban taron sauyin yanayi na MDD karo na 22 da ke gudana a birnin Marrakech na kasar Morocco.(Daily Trust)
Babban sifeto janar na 'yan sandan Najeriya Idris Ibrahim ya bayyana dalilan da suka kai ga kisan wasu 'yan shi'a da 'yan sanda suka yi ranar Litinin a Kano, biyo bayan wata arangama tsakanin sassan biyu.
Rahotanni na cewa, 'yan sanda kusan 4 da kuma 'yan shi'a 10 ne suka jikkata.(The Punch)