in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban bankin kasar Ghana zai samu bunkasa da zarar ya fara musayar kudin RMB da IMF ta lamunce
2016-11-23 10:35:36 cri

Kudin ruwan da babban bankin kasar Ghana zai samu zai iya karuwa ta hanyar amfani da tsarin musayar kudin RMB na kasar Sin bayan da Asusun ba da lamuni na duniya wato IMF ya amince da kudin Sin na RMB a matsayin kudin da ya shiga tsarin SDR.

Gwamnan babban bankin na kasar Ghana Abdul-Nashiru Issahaku, ya fadi hakan ne ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, ya zama wajibi a yi amfani da kudin na kasar Sin bisa la'akari da karuwar huldar kasuwanci dake tsakanin Ghana da kasar Sin.

Ya kara da cewa, ba shakka tattaunawa game da amfani da kudin RMB ta yi nisa, kuma da zarar an kammala shigar da kudin RMB cikin tsarin SDR, Ghana za ta ci gaba da musayar kudin ba tare da bata lokaci ba.

Gwamnan babban bankin ya yi alkawari da cewa, hukumomin kasar Ghana za su ci gaba da ta'ammali da kudin kasar Sin a hada-hadar cinikayya da takwarorinsu na kasar Sin.(Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China