Baki daya, wakilan jam'iyyun siyasa 7 ne suka zabarwa 'yan takarkarunsu gurabe a jikin kuri'un.
Jam'iyyar GCPP ce ta farko a jikin kuri'ar, sai PPP dake bi mata, sai kuma jam'iyyar NDC mai mulkin kasar.
Wannan ne karon farko da hukumar zaben kasar ta Ghana ta bada dama ga jam'iyyun kasar don zabar gurabe a jikin kuri'un da za'a kada a zaben kasar.
A watan Disamba ne al'ummar kasar Ghana za su fita rumfunan zabe, domin zabar shugaban kasa da mambobin majalisar dokokin kasar su 275.(Ahmad Fagam)