in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Au za ta tura tawagar masu sa ido a zabukan Ghana
2016-10-20 20:29:02 cri
Kungiyar tarayyar Afirka(AU) ta amince da tura wata tawagar masu sa-ido na dogon lokaci game da zaben kasar shugaban kasa da na 'yan majalisun dokokin kasar Ghana da aka shirya gudanarwa a ranar 7 ga watan Disamban wannan shekara.

Shugabar hukumar zartarwar kungiyar Madam Nkosazana Dlimini Zuma wadda ta bayyana hakan cikin wata sanarwar da aka rabawa manema labarai a jiya Alhamis, ta bayyana cewa, daukar wannan mataki ya biyo bayan gayyatar da gwamnatin kasar ta Ghana ta mikawa kungiyar ce.

Sanarwar ta ce, ana saran tura tawagar ce a ranar 20 ga watan Oktoba, kuma za ta kasance a kasar har zuwa lokacin da za a sanar da sakamakon karshe na zabukan kasar.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China