in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar zaben kasar Ghana ta sanar da sunayen 'yan takarar shugabancin kasar
2016-11-10 09:31:49 cri

Hukumar zaben kasar Ghana(EC) ta sanar da cewa, ta wanke sunayen mutane 7 wadanda za su tsaya takarar shugabacin kasar na ranar 7 a watan Disamban wannan shekara.

Bugu da kari, hukumar ta karbi karin takardun wasu 'yan takara guda uku, bayan da kotun kolin kasar ta ba da umarnin sake ba su wata dama ta gyara takardunsu na neman tsayawa takara. Wadannan 'yan takara uku, su ne Papa Nduom na jam'iyyar PPP, da Nana Konadu Agyeman-Rawlings ta jam'iyyar NDP da Edward Mahama na jam'iyyar PNC.

Yanzu ke nan,wadannan 'yan takara uku za su hade da sauran 'yan takara hudu da tuni aka amince su tsaya takarar shugabancin kasar, wato John Dramani Mahama na jam'iyyar NDC mai mulki, da Nana Akufo-Addo dan takarar babbar jam'iyyar adawa ta NPP. Sauran sun hada da Ivor Kobina Greenstreet na jam'iyyar CPP da kuma Jacob Osei Yeboah dan takara mai zaman kansa.

Haka kuma hukumar zaben ta yi watsi da takardun 'yan takara 8 da aka mika mata, yayin da 'yan takara biyu kuma suka janye.

Shugabar hukumar zaben kasar ta Ghana Charlotte Osei ta shaidawa manema labarai cewa, an soke tsayawar 'yan takarar ne , saboda ba su cika dokokin da suka shafi zabukan wannan shekara ba.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China