in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Ghana ya baiwa masu zuba jari a kasar tabbaci gabanin babban zaben kasar
2016-11-15 11:24:51 cri
Shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama, ya baiwa 'yan kasuwa da masu zuba jari a kasar kwarin gwiwa gabannin fara babban zaben kasar dake tafe a watan Disamba.

Shugaban ya basu tabbacin samun zaman lafiya da kyakkyawan yanayin kasuwanci a kasar, gabanin gudanar da babban zaben kasar dake tafe a watan gobe, wanda shugaba Mahama ke sake yin takarar neman zarcewa a shugabancin kasar.

Game da koma bayan tattalin arziki dake addabar duniya kuwa, shugaban yace, kasar Ghana ta samu nasarori masu yawa wajen kaucewa fuskantar matsin tattalin arziki, inda ta sha gaban kasashen duniya da dama, ya kara da cewa, kasar na cigaba da daukar matakan da suka dace domin kaucewa fadawa cikin tabarbarewar al'amurra.( Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China