in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan majalisun Ghana na bukatar ayyukan kyautata jin dadin jama'a bayan wa'adinsu
2016-11-03 10:16:11 cri
'Yan majalisun dokokin kasar Ghana sun bukaci a ranar Laraba da a kafa wani asusun fensho domin 'yan majalisu ta yadda za a taimaka musu bayan kammala wa'adinsu. Wannan zai taimaka a cewarsu ga 'yan majalisu dasu rike yanayin zaman rayuwa cikin wadata. Wa'adin 'yan majalisun dokokin kasar na yanzu zai zo karshe a ranar 6 ga watan Janairun shekarar 2017 da tsakiyar dare, a jajibirin rantsar da sabuwar gwamnati. Yawancin 'yan majalisun, musammun ma wadanda suka bar mukaminsu, na nuna damuwa tun tuni da matsalolin da suke fuskanta wajen samun aiki bayan tafiyarsu daga majalisar dokoki. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China