Ministan wanda ya bayyana hakan yayin zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua, ya ce, matakin asusun IMF na sanya RMB cikin tsarin na SDR abin a yaba ne, idan aka yi la'akari da rawar da kasar Sin ta ke takawa a fannin tattalin arzikin duniya.
Ya ce, tun kafin asusun na IMF ya yanke shawarar sanya kudin na RMB cikin wannan tsari, kasar Ghana ta dade tana tunanin amfani da kudin RMB a harkokin cinikayya da tattalin arzikin kasar. Ministan ya kuma ce, hakan zai rage matsalolin da 'yan kasuwan kasar suke fuskanta a harkokin su na saye da sayarwa, baya ga kara bunkasa harkokin cinikayya tsakanin Sin da Ghana
A cikin watan Satumban wannan shekarar ce, asusun na IMF ya sanar da sanya kudin na RBM cikin rukunin kudaden da za a rika amfani da su a tsarin musayar kudaden katare wato SDR a takaice.(Ibrahim)