Gwamnatin Najeriya ta ce, ta samu nasarar ceto mutane a kalla 50 da aka yi yunkurin yin safarar bil'Adama da su a kwanaki 4 da suka gabata a jahar Kano dake shiyyar arewa maso yammacin kasar.
Shehu Umar, shi ne kwamandan hukumar yaki da msau safarar bil'Adama na jahar (NAPTIP), ya sheda wa 'yan jaridu cewa, hukumar shigi da fici ta Najeriya ce ta ceto mutanen a jahar Katsina a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa Turai ta hanyar kasashen Nijer da Libya.
Ya kara da cewa, mutanen da aka ceto sun hada da mata da kananan yara, kuma sun fito ne daga jahohin Abia, Delta, Edo, Enugu, Imo da jahar Kwara.
Umar ya fada wa manema labarai cewa, ofishin hukumar ya ceto kimanin mutane 343 cikin wannan shekara, da suka hada da mata 221 da maza 122.
Ya ci gaba da cewa, jami'an sun gano mutanen ne ta hanyoyi uku, da suka hada da rashin cikakkun takardu, da rashin isasshen guzuri, da kuma bi ta barauniyar hanya. (Ahmad)