Nijar da Najeriya na tafiyar da huldar dangantaka da abokantaka a karkashin kwamitin hadin gwiwar dangantaka ta tsawon shekaru fiye da arba'in.
Baya ga batun yaki da kungiyar Boko Haram, shugabannin biyu zasu tattauna batutuwan tattalin arziki dake jan hankalin kasashen biyu, har ma da wasu batutuwan dake shafar nahiyar Afrika da ma duniya a halin yanzu, a yayin wannan ziyara, in ji wata mijiya mai tushe a birnin Yamai.
Musammun ma game da batun yaki da 'yan ta'addan Boko Haram, rundunar sojojin Nijar ta shiga Najeriya, a cikin rundunar hadin gwiwa tare da sauran rundunonin kasashen Chadi, Kamaru da Najeriya domin kawar da wannan annoba.
A cewar wasu hasashen alkaluma na kafofin yammacin duniya, dalilin matsalar Boko Haram, kusan mutane dubu 20 aka kashe kana fiye da mutane miliyan 2.6 suka kaura daga muhallinsu tun daga shekarar 2009.
A Nijar, yankin jihar Diffa dake kudu maso gabashi, mai iyaka da Najeriya, ya kasance wani fagen daga tun yau da shekaru biyu, kuma munanan hare haren kungiyar Boko Haram tun daga sansanoninta dake Najeriya, sun yi sanadiyyar mutuwar daruruwan fararen hula da sojoji da janyo miliyoyin 'yan gudun hijira na Nijar da na Najeriya. (Maman Ada)