Karamin ministan albarkatun man fetur a Najeriya Ibe Kachikwu, ya ce yanayin da ake ciki na barnata kayayyakin kamfanonin mai a yankin Niger-Delta dake kudancin kasar, ya haifar da babban koma-baya ga kasar. Mr. Ibe Kachikwu, ya ce gwamnatin na tattaunawa da jagororin yankin, a wani mataki na kawo karshen ayyukan tsagerun Niger-Delta.
A cewar ministan, ayyukan tsagerun yankin na haddasa asarar ganga kusan 600,000 na yawan mai da kasar ke hakowa a ko wace rana, inda a yanzu jimillar gurbataccen mai da ake hakowa bai wuce ganga miliyan 1.65 a ko wace rana ba.
Sai dai a daya bangaren, ministan ya ce, gwamnatin kasar mai ci na daukar matakan fadada hanyoyin bunkasa tattalin arziki, ta wasu karin hanyoyi da ba na cinikayyar man fetur ba. (Saminu)