A yau Litinin ne, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya aika wasikar taya murnar cika shekaru 50 da kafa kungiyar raya masana'antu ta MDD wato UNIDO.
A cikin wasikar, Li Keqiang ya ce, kasar Sin tana kira ga kasashen duniya da su kara yin hadin gwiwa a fannin sarrafa kayayyaki, a kokarin ganin sun taimakawa juna domin samun moriyar juna da nasara tare, tare da lalubo bakin zaren inganta sabuwar hanyar hada kan kasashe maso tasowa da kuma hada kan kasashe maso tasowa da masu ci gaba.
Firaministan kasar Sin ya kara da cewa, a matsayinta na kasa mai tasowa mafi girma a duniya, kasar Sin za ta ci gaba da mara wa kungiyar UNIDO baya. (Tasallah Yuan)