A yau ne firaministan kasar Sin Li Keqiang ya halarci taron majalisar shugabannin gwamnatocin kasashe mambobin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai wato SCO a birnin Bishkek, hedkwatar kasar Kyrgyzstan.
A yayin taron, Li Keqiang ya ba da shawarwari da dama kan yadda mambobin kungiyar ta SCO za su hada kansu domin samun ci gaba. Da farko dai, za a samar da muhalli mai zaman lafiya da kwanciyar hankali. Na biyu, raya tattalin arziki cikin hadin gwiwar mambobin kungiyar. Na uku, daga matsayin hadin gwiwa ta fuskar kera kayayyaki. Na hudu, za a fito da sabuwar damar yin hadin gwiwa. Na biyar, za a kyautata tsarin tattarawa da zuba jari a shiyyar. Na karshe, za a inganta yin mu'amala ta fuskar al'ada.
Firaministan kasar Sin ya yi nuni da cewa, kasar Sin na son hada kai da sassa daban daban wajen kara azama wajen ganin jama'ar shiyyar sun ci gajiyar hadin gwiwar kungiyar ta SCO. (Tasallah Yuan)