in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang ya gana da shugaban kasar Kyrgyzstan
2016-11-03 11:24:23 cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gana da shugaban kasar Kyrgyzstan Almazbek Atambayev da daren jiya Laraba a fadar shugaban da ke Bishkek, babban birnin kasar.

Li Keqiang ya mika gaisuwar shugaban kasar Sin Xi Jinping ga shugaba Atambayev, sa'an nan ya bayyana cewa, a watan Yuni na bana, shugabannin kasashen biyu sun gana da juna a yayin taron koli na Tashkent, na kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai, inda suka cimma matsaya daya a fannoni da dama. Ya ce ko da yaushe kasar Sin na da aniyar raya dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, da inganta hadin kansu yadda ya kamata, bisa ka'idojin nuna girmama ga juna, da zaman daidai wa daida, da kuma cin moriyar juna da samun nasara tare.

A nasa bangaren kuma shugaba Atambayev ya furta cewa, kasar Sin kasa ce da ta nuna sahihin zumunci ga kasar Kyrgyzstan. Har wa yau kasar Sin ta ba ta taimako a fannin ci gaban ta, ba kuma tare da gindaya ko wane irin sharadin siyasa ba. Don haka kasarsa na matukar godiya ga Sin. Ya ce dukkan kasashen biyu na da aniyar inganta hadin gwiwarsu. Kuma Kyrgyzstan na fatan ci gaba da kokari tare da kasar Sin, wajen raya hadin kansu a fannonin zirga-zirga, da sadarwa, da sha'anin kudi da dai sauransu, a kokarin ciyar da dangantakar da ke tsakaninsu gaba. (Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China