Firaministan kasar Sin Li keqiang, ya yi karin haske game da shirin yaki da fatara na kasar Sin, yana mai cewa, za a maida hankali game wasu yankuna na musamman, wadanda suka kunshi na kan iyakokin kasar, da masu karancin ci gaba, dama wadanda al'ummun su ke cikin matsanancin halin matsi.
Wata sanarwa da aka fitar, ta rawaito Li Keqiang na jaddada muhimmancin shirin na yaki da fatara, yayin da yake jagorantar taron majalissar zartaswar kasar a ranar Talata. Firaministan ya ce, gwamnati za ta tabbatar da aiwatar da wasu shirye shirye, wadanda za su ba da damar kawar da talauci tsakanin al'umma nan da shekara ta 2020.
Ya ce, za a agazawa yankuna mafiya fama da talauci, wajen bude masana'antun da suka jibanci noma, da yawon shakatawa, da kuma na cinikayyar zamani. Kaza lika za a tabbatar da irin wadannan yankuna sun amfana daga ribar da ake samu daga albarkatun lantarki ta ruwa, da fannin hakar ma'adanai.
Gwamnatin kasar Sin dai na fatan Sinawa kimanin miliyan 30 dake sassan kasar daban daban, za su amfana daga shirin yaki da fatara yayin da ake dada raya kananan masana'antun kasar.(Saminu)