in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministocin Sin da Rasha sun shugabanci taron firaministocin Sin da Rasha karo na 21
2016-11-08 09:45:32 cri
A jiya Litinin da yamma ne firaministan kasar Sin Li Keqiang da takwaransa na kasar Rasha Dmitry Medvedev suka shugabanci taron firaministocin Sin da Rasha karo na 21 da ya gudana a fadar Constantine dake birnin St.Petersburg na kasar Rasha.

A jawabinsa, Li Keqiang ya bayyana cewa, Sin tana son hada kai tare da kasar Rasha, ta yadda za a karfafa shirin nan na "ziri daya da hanya daya" da kawancen tattalin arziki na Turai da Asiya, da raya dangantakar dake tsakanin Sin da Rasha, da hadin gwiwarsu, don samun moriyar juna da amfanawa jama'ar kasashen biyu. Li Keqiang ya yi nuni da cewa, sakamakon koma bayan tattalin arzikin da ake fuskanta, da raguwar saurin bunkasuwar harkokin ciniki a duniya, kamata ya yi Sin da Rasha su kara yin amfani da fiffikonsu, da ba da gudummawa, ta yadda za a samu ci gaba da kuma canja tsarin tattalin arzikinsu.

A nasa bangare, Medvedev ya bayyana cewa, Rasha da Sin abokan kasashe ne dake makwabtaka da juna. Rasha ta dora muhimmanci sosai kan sada zumunta da hadin gwiwa dake tsakanin kasashen biyu, kuma tana fatan za su aiwatar da abubuwan da suka cimma daidaito a kai, da yin amfani da tsarin hadin gwiwar dake tsakanin gwamnatocin kasashen biyu, da kuma sa kaimi ga raya hadin gwiwarsu a dukkan fannoni. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China