Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya tabbatar da cewa kasar ta yi nasarar aiwatar da muhimman ayyukan raya kasa na shekarar 2016, karkashin jagorancin shugaba Xi Jinping kuma sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminist ta kasar Sin.
Mista Li, ya bayyana hakan ne a yayin muhimmin taron tattaunawa game da yadda za a bunkasa ci gaban tattalin arzikin kasar Sin da inganta zaman rayuwar Sinawa.
Ya bukaci hukumomin da abun ya shafa da su mayar da hankali wajen samar da ayyukan yi, kana su ba da fifiko wajen bunkasuwar masana'antu domin ci gaban tattalin arziki, da bude kofa da kuma fasahar kirkire-kirkire.