in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin ya gana da shugaban kasar Rasha
2016-11-09 09:36:58 cri

Da yammacin jiya Talata firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya gana da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a birnin Moscow, hedkwatar kasar Rasha.

A yayin ganawar tasu Li Keqiang, ya ce Sin da Rasha kasashe ne mafiya kusanci da juna ta fuskar makwabtaka, wadanda suka kafa huldar abokantaka ta hadin gwiwa daga dukkan fannoni a tsakaninsu. Suna ta raya huldarsu da hadin gwiwarsu yadda ya kamata, lamarin da ya rika samun sabbin sakamako. Hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Rasha ba kawai tana amfanawa juna ba, har ma tana da amfani wajen tabbatar da zaman lafiya, kwanciyar hankali, ci gaba da wadata a shiyyar da suke ciki da ma duk duniya baki daya. Ya kamata kasashen 2 su aiwatar da ra'ayi daya da shugabanninsu suka cimma, a kokarin kara raya huldarsu zuwa sabon mataki.

A nasa bangaren, mista Putin ya ce, kasashen Rasha da Sin suna kara yin mu'amala da juna, kana gwamnatocin kasashen 2 suna hada kansu yadda ya kamata. Shawarwarin da firaministocin kasashen 2 suke gudanarwa a lokaci-lokaci ya kara inganta bunkasuwar hadin gwiwar kasashen 2. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China