in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Djibouti ya gana da mataimakin shugaban Sin
2016-11-18 11:22:20 cri
Jiya Alhamis, shugaban jamhuriyar kasar Djibouti, kana shugaban jam'iyya mai mulkin kasa ta kawancen jama'a mai neman ci gaban kasa Ismail Umar Guelleh, ya gana da mataimakin shugaban kasar Sin Li Yuanchao a fadar shugaban kasar dake Djibouti.

A yayin ganawar tasu, Li Yuan Chao, ya bayyana cewa, ra'ayin daya da shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugaba Guelleh suka cimma a yayin taron koli na dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka da aka yi a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu, ya ba da jagoranci kan raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Kana a halin yanzu, an samu babbar dama ta raya hadin gwiwa a tsakanin kasar Sin da Djibouti, shi ya sa kasar Sin take son hada kai da kasar Djibouti wajen aiwatar da sakamakon da aka cimma a taron koli na Johannesburg, ta yadda za a karfafa fahimtar siyasa a tsakanin bangarorin biyu, yayin da habaka hadin gwiwar kasashen biyu a fannoni daban daban yadda ya kamata, domin ciyar da dangantakar diflomasiyya a tsakanin kasashen biyu gaba.

Haka zalika, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin tana son kara yin shawarwari da hadin gwiwa da jam'iyyar kawancen jama'a mai neman ci gaba ta kasar Djibouti, domin zurfafa mu'amalar dake tsakanin kasashen biyu.

A nasa bangaren, shugaba Guelleh ya bayyana cewa, zumuncin dake tsakanin kasar Sin da kasar Djibouti yana da dogon lokaci, kasar Sin ita ce abokiyar arziki ta kasar Djibouti, wadda kasar Djibouti take dogara kanta. Haka kuma, shirye-shiryen hadin gwiwar Sin da Afirka guda goma, da shirin zirin tattalin arziki na hanyar siliki da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya fitar, sun ba da damammaki masu kyau ga kasar Djibouti wajen neman bunkasuwa, shi ya sa kasarsa take son karfafa shawarwari da hadin gwiwar dake tsakaninta da kasar Sin, ta yadda za a ci moriyar juna.

Bugu da kari, ya kara da cewa, dangantakar dake tsakanin jam'iyyar mai mulkin kasar ta Djibouti, da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta ba da muhimmanci wajen karfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, don haka, jam'iyyar kawancen jama'a mai neman ci gaba ta kasar Djibouti tana sa ran karfafa mu'amalar dake tsakaninta da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China