in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin Huawei na Sin zai zuba jari a bangaren makamashin hasken rana a Djibouti
2016-07-21 09:55:06 cri
Babban kamfanin sadarwar nan na kasar Sin, Huawei, zai zuba jari a bangaren makamashin hasken rana a Djibouti, in ji wata sanarwar ma'aikatar makamashin kasar Djibouti a ranar Laraba. Wannan sanarwa ta zo bayan karbar wata tawagar kamfanin kasar Sin a karkashin jagorancin darekta janar na wannan kamfani, mista Qiu Yulong, da ministan makamashin Djibouti da albarkatun muhalli, mista Yacin Houssein ya yi a wannan ranar.

A cewar wannan sanarwa, bangarorin biyu sun tattauna sosai kan damammakin ci gaba na huldar dangantakar tattalin arziki da ta kasuwanci a bangaren makamashi.

Musammun ma sun cimma ra'ayin aza ginshiken wannan dangantaka ta hanyar kafa wani shirin farko a bangaren sabbin makamashi musamman ma a bangaren hasken rana. A ganin darekta janar na Huawei, wannan shi ne na zuba jari a bangaren sabbin makamashi da ake samu sosai a kasar Djibouti. Dalilin kwanciyar hankali ta fuskar siyasa da bunkasuwar tattalin arziki dake karuwa, kasar Djibouti ta kasance a yau wata kasar dake jan hankalin masu zuba jari na kasashen duniya baki daya.

Bayan fasahohin sadarwa na TIC, da muke ci a Djibouti tun yau da 'yan shekaru, muna kuma fatan ba da gudunmuwa ga ci gaban bangaren makamashi a wannan kasa, in ji mista Yulong.

A nasa bangare, ministan makamashin Djibouti, Yacin Houssein, ya nuna cewa wannan shiri na cikin jadawalin siyasa na bunkasa makamashi na shugaban kasar Djibouti, Ismail Omar Guelleeh, domin samar da makamashi mai tsabta na dindindin, da kuma kowa a dukkan fadin kasar zai samu a cikin farashi mai rahusa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China