in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Djibouti ta shiga sabon kawancen soja na Larabawa domin yaki da ta'addanci
2015-12-16 11:10:27 cri
Kasar Djibouti ta bi sahun kasashe fiye da talatin da suka hada da Saudiyya, domin kafa wani kawancin soja na yaki da ta'addanci, a cewar kamfanin dillancin Labarai na Djibouti (ADI).

ADI ya bayyana cewa, wadannan kasashe sun yi kira ga sauran kasashen duniya da kungiyoyin kasa da kasa da su tallafa musu a kokarin da ake na yaki da ta'addanci ta yadda za a tabbatar da zaman lafiya da tsaro.

Har ila yau a cewar wannan majiya, cibiyar gudanar da ayyukan cikin hadin gwiwa na wannan sabon kawance soja na Larabawa za ta kasancewa a birnin Riyad na Saudiyya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China