in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Djibouti ya sake lashe zaben shugaban kasa
2016-04-11 11:24:17 cri
Ministan harkokin cikin gidan kasar Djibouti Hassan Omar Mohammad ya sanar a ran 9 ga wata cewa, shugaban kasar mai ci mista Ismail Omar Guelleh ya sake lashe zaben shugaban kasar da samun kuri'un da yawansu ya kai kashi 86.68 cikin 100 bisa jimillar kuri'un da aka jefa a zagaye na farko.

Bisa kididdigar da aka bayar, an ce, dan takarar jam'iyyar People's Rally for Progress mai mulki wato Ismail Omar Guelleh ya samu yawan kuri'u da kashi 86.68 bisa dari, lamarin da ya ba shi damar shiga gaban dukkan abokan hamayyarsa da babban rinjaye. Masu kada kuri'a da yawansu ya kai kashi 68 cikin 100 ne suka kada kuri'unsu a cikin zaben shugaban kasar a wannan karo .

Wannan shi ne karo na hudu da mista Guelleh mai shekaru 68 ya lashe zaben tun shekarar 1999, inda zai kuma fara wa'adin aikinsa na biyar na shugaban kasa. A cikin jawabinsa, Mr. Guelleh ya ce, yana sane da bukatun al'ummomin kasar kware da gaske kuma zai dukufa wajen warware su, zai kuma fuskantar da kalubaloli iri daban daban tun daga wannan rana da ya sake hau kan kujerar shugabanci, musamman ma kan matsalolin da suka shafi guraben aikin yi da matsalar sayen gidaje. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China