in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manzon musamman ta shugaba Xi Jinping ya halarci bikin rantsar da shugaban Djibouti
2016-05-09 10:04:28 cri
A jiya Lahadi 8 ga watan ne manzon musamman ta shugaban kasar Sin Xi Jinping, kana mataimakiyar shugabar zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Yan Junqi, ta halarci bikin rantsar da shugaban kasar Djibouti, Ismail Omar Guelleh a fadar gwamnatin kasar dake birnin Djibouti.

Kafin bikin rantsuwar, Mr. Ismail Omar Guelleh ya gana da Madam Yan a fadar shugabar sa, inda Madam Yan ta isar da sakon murna da fatan alheri na shugaba Xi ga shugaban na Djibouti.

Madam Yan ta furta cewa, Sin tana darajanta dankon zumunci dake tsakanin kasashen biyu, tana kuma fatan za a karfafa hadin gwiwar moriyar juna da sada zumunci tsakanin sassan biyu a fannoni daban daban, da zummar daga matsayin dangantakar dake tsakaninsu zuwa wani sabon mataki.

A nasa bangare, mista Guelleh ya yi godiya ga shugaba Xi bisa tura manzonsa na musamman don halartar bikin rantsar da shi a matsayin shugaban kasa, ya kuma bayyana cewa, Sin muhimmiyar aminiya ce ta Djibouti, a sabili da haka, kasar ke fatan zurfafa hadin gwiwa da sada zumunci tsakaninta da Sin a duk fannoni.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China