A jiya Alhamis ne kasar Sin ta harba kumbon gwaje-gwaje na Tiangong-2 zuwa sararin samaniya cikin nasara.
Dangane da hakan ne kuma shahararriyar mujallar Halittu ta "Nature" da ake wallafawa a kasar Birtaniya, ta bayyana cewa, na'urorin gwaje-gwajen kimiyya da kumbon ke dauke da su, kasashen Sin da Turai ne suka sarrafa su cikin hadin gwiwa.
Mujallar ta ce, sakamakon gudanar da karin irin wadannan ayyuka cikin hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen waje, ya sa kasar Sin kasancewa wuri da ke iya faranta rayukan masu ilmin kimiyyar sararin samaniya na kasa da kasa, a fannin gwajin ilmin kimiyyar sararin samaniya. (Tasallah Yuan)