Sanarwar ta bayyana cewa, zaben raba gardama din muhimmin aiki ne wajen kawo karshen lokacin mulkin wucin gadi na kasar Afirka ta Tsakiya, wanda zai aza tubali wajen tabbatar da zaman lafiya a kasar. Ban Ki-moon ya jaddada cewa, MDD na nuna goyon baya ga hukumomin wucin gadi na Afirka ta Tsakiya da su yi kokari wajen aiwatar da ayyuka da yunkurin yin zabe a kasar.
Kasar Afirka ta Tsakiya za ta yi zaben raga gardama kan sabon daftarin tsarin mulkin kasar a ranar 13 ga wata. An ce, bayan makwani biyu, za a yi zaben shugaban kasar da na majalisar dokoki da aka jirkirtar da su sau da dama. (Zainab)