Game da hakan, mataimakin shugaban tawagar ta MINUSCA Diane Corner, ya ce tawagar ta samu rahoton wannan zargi ne a ranar 12 ga wata cewa, wasu ma'aikatan tawagar 3 sun ci zarafin mata ciki har da wata yarinjiya.
Mai bada taimako ga babban sakataren MDD Vannina Maestracci ya bayyana cewa, MDD ta riga ta sanar da hakan ga kasashen da suka tura wadannan ma'aikatan kiyaye zaman lafiya, inda ake sa ran kasashen za su tsaida kudurin ko za a gudanar da bincike kan su ko kuma a'a.
Jami'in ya kara da cewa, idan kasashen da suka tura ma'aikatan kiyaye zaman lafiyar ba su yi bincike kan lamarin ba, ko suka gaza bada amsa har tsawon kwanaki 10, MDD za ta kaddamar da nata bincike ba tare da wani bata lokaci ba. (Zainab)