Mr. Ban ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya bayar a jiya Lahadi ta hannun kakakinsa.
Sanarwar ta ce, Ban Ki-moon ya bayyana kwarin gwiwarsa yadda 'yan kasar kimanin miliyan 2 ne suka yi rajista domin kada kuri'u. Don haka, ya bukaci bangarori daban daban na kasar da su hada kai da tawagar musamman ta MDD dake kasar, domin ganin an magance da duk wata matsala da ka iya kawo cikas wajen gudanar da zaben cikin lumana bisa doka.
Bugu da kari, Ban Ki-moon ya nuna yabo ga gwamnatin wucin gadin kasar bisa shirya zaben raba gardama game da kundin tsarin mulkin kasar da ya gudana a farkon watan nan da muke ciki. Ya kuma bayyana cewa, MDD za ta ci gaba da taimaka wa kasar a kokarin da take na tabbatar da zama lafiya da kwanciyar hankali. (Maryam)