Mista Carmon ya bayyanawa 'yan jarida ta wayar tarho cewa, ya yi Allah wadai da tada rikicin wanda aka yi shi don hargitsa babban zaben kasar, amma ya tabbatar da cewa, yanzu an samu zaman lafiya a kasar. Firaministan ya yi nuni da cewa, watakila kungiyar dake yunkurin kawo illa ga babban zaben kasar ce ta tada rikicin, domin ta san ba za ta samu ikon mulki ta hanyar zaben ba.
Bayan faruwar rikicin, an yi kira da a gyara jadawalin harkar siyasa a kasar Afirka ta Tsakiya, ciki har da jinkirtar da zaben shugaban kasar da na majalisar dokokin kasar da ake shirin gudanar da su a ranar 18 ga watan Oktoba. Kuma wasu na bukatar da a kada kuri'ar jin ra'ayoyin jama'a game da tsarin mulkin kasar a ranar 4 ga watan Oktoba. (Zainab)