Ministar tattalin arzikin fasahar zamani, madam Cina Lawson, ta kaddamar a ranar Litinin da ayyukan bikin makon kasa da kasa kan harkokin kasuwanci a kasar Togo.
Wannan biki shi ne karo na bakwai a bangaren kasa da kasa, amma a karon farko ne da ake gudanar da wannan makon kasa da kasa kan harkokin kasuwanci a kasar ta Togo, bikin da ake gudanarwa daga ranar 14 zuwa 20 ga watan Nuwamba a wannan kasa. (Maman Ada)