in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta sanar da shirya wani taron musammun kan tsaron teku a Togo
2016-10-09 13:18:39 cri
Kungiyar tarayyar Afrika (AU) ta sanar a ranar Asabar cewa wani zaman taron musamman kan tsaron teku, tsaro da ci gaba a nahiyar Afrika, zai gudana a ranaar 11 zuwa 12 ga watan Oktoba a birnin Lome na kasar Togo.

Nkosazana Dlamini Zuma, shugabar kwamitin tarayyar Afrika (AU), da shugaban Togo Faure Gnassingbe sun yi taro a ranar Laraban da ta gabata a birnin Addis Abeba na Habasha, inda suka tattauna batutuwan shiye shiryen wannan taro, a cewar wata sanarwar AU.

Shugabannin biyu sun jaddada muhimmancin tsamowa cikin albarkatun take domin kara bunkasa ci gaban Afrika, maimakon barin wadannan albarkatun kasancewa wani tushen yake-yake.

Taron zai amince da wani daftarin tsaro na Afrika kan teku, in ji sanarwar, sakamakon haka, shugabannin kasashe da gwamnatoci za su halarci shawarwarin da za su zarce batun tsaro kawai domin shigar da batutuwan da suka hada da kamun kifi, sufuri, ma'adinai da yawon bude ido, lamarin da zai taimaka wajen kafa ayyukan yi a Afrika.

Shugaba Faure Gnassingbe ya kai ziyarar aiki ta kwanaki biyu a kasar Habasha, inda a yayin ta, shugaban Togon ya tattauna tare da shugabar kwamitin AU kan ina aka kwana game da batun shirye shiryen taron na musammun. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China