Qian Lihua ya bayyana hakan ne yayin taron tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Afirka wanda ke gudana a birnin Lome. Ya kuma gabatar da wasu shawarwari kan yadda za a yaki 'yan fashi teku a yankin tekun Guinea.
Bugu da kari, ya ce kasar Sin za ta shiga a dama da ita a kokarin da kasashen duniya suke yi na yaki da 'yan fashin teku a yankin tekun Guinea, ta hanyar taimakawa kasashen da ke shiyyar wajen gina wasu muhimmman kayayyakin more.(Ibrahim)